Rundunar Sojin Najeriya ta mika mata 778 da yara da dama da ta kwato a samamen da ta kaiwa ‘yan ta’ addan Darul Salam.

A lokacin da yake karban wadanda aka kubutar, mataimakin Gwamnan jihar Emmanuel Akabe Ya bukaci ‘yan ta’ addan dake tserewa sakamakon matsin lamba da suke fuskanta su mika wuya ga rundunar sojin Najeriya.

Mataimakin Gwamnan wanda ya wakilci gwamnan jihar ya shawarci ‘yan ta’ addan su mika makaman su domin maido da zaman lafiya da tsaro a jihar.

Matan da yara da aka kwato iyalai ne na ‘yan ta’ addan da suka kafa sansanoni a dajin Uttu dake karamar hukumar Toto dake jihar.

Daga cikin matan da aka kwato akwai matan 86 da yara 232 da suka fito daga jihar Nijer, sai mata 20 da yara 64 daga jihar Kano, yayin da jihar Nasarawa ke biye da mata 8 da yara 11.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *