Gwamnatin tarayya ta bukaci gwamnatocin jihohin da suke shirye-shiryen bude makarantu su yi taka-tsantsan, domin cutar korona na nan a matsayinta na cuta mai hadarin gaske.

Shugaban kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin yaki da cutar kuma Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, ya bada gargadin a lokacin da yake magana a wajen taron da kwamitin ke shiryawa a Abuja.

Ya ce a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke daukar matakan bude sauran bangarori da aka rufe a baya, akwai bukatar al’ummomi su rika bin matakan kariya, wanda a cewarsa hakan zai sa a yaki cutar baki daya. 

Mustapha ya ce kwamitin zai gabatarwa shugaban kasa Muhammadu Buhari rahoton wucin gadi karo na 7, domin daukar matakan da suka kamata a dauka a gaba.

Ya kara da cewa za a bayyana sabbin matakan da suka kamata a dauka a ranar Alhamis 3 ga wannan watan na Satumba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *