Ministan lafiya Osagie Ehanire, ya ce an samu raguwar gwaje-gwajen da ake na cutar korona a fadin Najeriya sakamakon karancin samfuri da ake turawa daga jihohi da dama dake fadin Najeriya.

Ehanire ya bayyana hakan ne a wajen taron kwana guda-guda da kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin yaki da cutar ke shiryawa a Abuja.

Ehanire ya bada misali da jihar da ta yiwa mutane dubu 35 gwajin cutar korona a watan Yuli, ta yiwa mutane dubu 20 ne kacala a watan Augustan da ta gabata.

Yayin da a wata jiha ta daban da a baya ta yiwa mutane dubu 23 gwajin yanzu ta yiwa mutane dubu 4 ne kacal a watan Augusta.

Ministan ya bukaci jihohi da su kara zage damtse wajen ci gaba da sanya ido tare da gwaje-gwajen cutar a lugu da sako na kananan hukumomi domin tabbatar da yakar cutar baki daya.

Ya kara da cewa yawancin dakunan gwaje-gwajen da ake dasu a jihohi basu cikka sharuddan da ake bukata ba, kuma akwai shirye-shirye da aka yi domin inganta su nan gaba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *