Gwamnatin tarayya ta ce za ta ware naira bilyan 600 domin taimakawa kanana da matsakaitan manoma, domin karfafa musu gwiwa.

Ministan kula da harkokin noma da raya karkara Sabo Nanono, ya bayyana haka, ya ce gwamnatin za ta dau wannan matakin ne a daidai wannan lokaci da annobar COVID-19 ta shafi fannoni da dama.

Ya ce bunkasa harkar noma na daga cikin muhimman kudurorin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya a gaba, da zummar kai Najeriya matakin ciyar da kanta da kuma makwafta.

Sai dai matsalar tsaro na daga cikin kalubalen da bangaren kula da harkokin noma ke fuskanta a fadin Najeriya musamman yankunan karkara.

Haka kuma kungiyar Amnesty International ta zargi hukumomin tsaro da gazawa wajen ba mazauna yankunan karkara tsaro, inda ‘yan bindiga suke hanasu zuwa gonaki.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *