Gwamnatin jihar Kwara ta bukaci taimakon hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC wajen kwato wasu kudaden almundahana.

Antoji Janar na jihar kuma kwamishinan shari’a Salman Jawondo, ya mika bukatar a lokacin da ya jagoranci tawagar ma’aikatar shari’a zuwa ofishin hukumar dake jihar.

Ya ke hukumar EFCC hukuma ce dake da tasirin gaske a yaki da cin hanci da rashawa.

Jawondo ya ce a shirye ma’aikatar shari’ar jihar take ta ba hukumar hadin gwiwa da goyon bayan da take bukata wajen yaki da masu sama da fadin da dukiyar kasa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *