Rundunar sojin Kamaru sun kaiwa ‘yan aware a garin Boyo dake arewa maso yammacin kasar hari, inda suka yi nasarar halaka mayaka 17, tare da kama wasu guda 7.

An dai sanar da wannan nasara ce cikin labaran kafar radiyon gwamnatin Kamaru.

Dakarun na Kamaru sun kuma bankado wani wajen ajiye makamai masu fashewa da kuma shagon dinka kakin soji.

Dakarun na Kamaru sun kai harin ne ranar Asabar 30 ga watan Agustan da ya gabata a Fundong dake yankin arewa maso yammacin kasar masu amfani da harshen turanci.

Harin na zuwa ne a dai dai lokacin da aikata laifuka da garkuwa da mutane ke ci gaba da yin kamari a yankunan 2 masu amfani da harshen turancin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *