Gwamna Matawalle na jihar Zamfara, ya ce gwamnatin sa za ta kafa hukuncin kisa ga direbobi masu tukin ganganci a jihar.

Hakan dai ya na zuwa ne, bayan mutuwar wasu magoya bayan sa 15 sakamakon wani hatsarin mota bayan sun yi masa maraba da zuwa karamar hukumar Tsafe.

Hatsarin dai ya auku ne yayin da wata babbar mota ta kwace, sannan ta bugi ayarin motoci hudu na magoya bayan Matawalle ke ciki a kan hanyar Gusau zuwa Funtua.

Daraktan labarai da wayar da kan al’umma na gwamnan Yusuf Idris, ya ce za a samar da hukuncin kisa a matsayin matakin hukunta direbobi masu tukin ganganci.

Ya ce gwamnan ya yanke hukuncin ne, lokacin da ya jagoranci ‘yan majalisar sa da hukumar kamfanin BUA a wata ziyarar jaje da su ka kai fadar sarkin Gusau Ibrahim Bello game da mutuwar mutanen 15.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *