Tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya karyata batun cewa zai bar jihar Laga domin komawa garin Azare da ke jihar Bauchi, inda kakan sa marigayi Sarki Muhammadu I ya zauna lokacin da sardauna ya tsige shi.

Sarki Sanusi ya ce maimakon komawa Azare kamar yadda waasu ke hasashe a shafukan sada zumunta, zai koma jami’ar Oxford da ke kasar Ingila.

Idan dai ba a manta ba, an ruwaito cewa tsohon sarki Sunusi na shirye-shiryen komawa Azare da zama na din-din-din, lamarin da ya ce babu kashin gaskiya a ciki.

Sai dai ya yarda cewa mutanen Azare sun gabatar masa da bukata, inda suka nemi ya dawo da zama nan kamar kakansa, marigayi Muhammadu Sanusi I.

Da ya ke magana a madadin Sanusi, daya daga cikin ‘yan  majalisar sa, ya ce masarautar Azare ta tuntube shi a kan sauya mazauni da ake has ashen, amma ya ki cewa uffabn a kan haka, sai dai ya tabbatar da cewa ya na shirin komawa jami’ar Oxford da ke Ingila.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *