Kungiyar Kwato Hakki da Sa-ido a Kan Hana Rashawa SERAP, ta maka Shugaba Muhammadu Buhari a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda ta nemi a tilasta wa Shugaba Buhari ya bayyana sunayen wadanda gwamnatin sa ta kwato naira biliyan 800 daga hannun su.

Idan dai ba a manta ba, yayin da ya jawabi a wajen bikin ranar Dimokradiyya, shugaba Buhari da bakin shi ya ce gwamnatin sa ta kwato naira biliyan 800 daga hannun barayin gwamnati, kuma ana ci-gaba da zuba kudaden a cikin ayyukan raya kasa da gwamnati ke gudanarwa.

Cikin karar da SERAP ta shigar, ta nemi kotu ta tilasta Buhari ya bayyana sunayen barayin gwamnati da aka kwato naira biliyan 800 a hannun su, a kuma san naira nawa aka kwato daga kowane mutum daya.

Kungiyar, ta kuma nemi  Shugaba Buhari ya bayyana dukkan ayyukan da ya ce an yi da kudaden da kuma inda aka yi ayyukan, sannan ya bayyana farashin da aka bada kowace kwangilar da aka biya a cikin kudaden.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *