Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta dauki mataki game da rikicin kudancin jihar Kaduna.

Farfesa Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin shugaba Buhari ba za ta yi watsi da manyan batutuwan da su ka jawo rigimar da ake yi a yankin na kudancin jihar Kaduna ba.

Osinbajo ya bayyana haka ne, a lokacin da ya yi jawabi a wajen babban taron shekara-shekara na kungiyar lauyoyin Nijeriya a makon da ya gabata.

Mataimakin shugaban kasar, ya ce maida wasu saniyar ware da aka na daga cikin musabbabin rikicin.

Ya kuma bayyana rashin hukunta wadanda aka samu da laifin kashe Bayin Allah a matsayin daya daga cikin abubuwan da ke kara hura wutar rikicin.

Osinbajo, ya ce akwai bukatar gwamnati ta tabbatar an yi wa al’umma adalci don a samu zaman lafiya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *