Gwamnatin Kano ta kashe naira biliyan 3 da miliyan 400 wajen aiwatar da shirin wajabtawa da kuma bada ilimi kyauta a jihar.

Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana ya bayyana haka a lokacin gabatar da takardar kudi ta naira miliyan 20 ga kananan hukumomi 44 da ke jihar a ranar Asabar, wanda jimillar kudaden su ka tasamma naira miliyan 880.

Ya ce an yi rabon kudaden ne domin yin kari a shirin gyaran makarantun firamare da sakandare da kefadin jihar, sannan ganduje ya ce gwamnatin sa ta ware sama da kaso 26 cikin 100 na kasafin kudin ta ga sashin ilimi, wanda ya yi dai-dai da amincewar hukumar kula da ilimi ta duniya UNESCO.

Gwnduje ya kara da cewa, sun yi nasarar samar da kudaden ne ta hanyar bada kashi 5 cikin 100 na kudaden shigar jihar, da kuma karin kashi 5 cikin 100 na kudaden kananan hukumomi, da kashi 2 cikin 100 na duk wata kwangila da aka bada a jihar, da dai sauran su.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *