Kotun Ƙoli ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kogi Musa Wada ya daukaka, inda ya ke kalubalantar nasarar Gwamna Yahaya Bello na jam’iyyar APC.

Jagoran alkalan da su ka yanke hukuncin kuma shugaban alkalan Nijeriya Tanko Muhammad, ya ce masu kara sun gaza gabatar da kwakkwarar hujjar da za ta tabbatar da zargin su, don haka ta tabatar da Yahaya Bello a matsayin wanda ya samu nasara a zaben gwamnan jihar da ya gabata.

Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC ce ta sanar da Yahaya Bello na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya samu nasara a zaben da aka yi a watan Nuwamba na shekara ta 2019.

Yahaya Bello dai ya samu kuri’u dubu 406 da 222, yayin da Musa Wada na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u dubu 189 da 704, sai kuma Natasha Akpoti ta jam’iyyar SDP da ta samu kuri’u dubu 9 da 482.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *