Ministan Ƴada labarai na kasar Ghana Kojo Nkrumah, ya karyata korafin da ministan Ƴada labarai na Nijeriya Lai Mohammed ya yi na zargin gwamnatin kasar da muzguna wa ‘yan Nijeriya.

Idan dai ba a manta ba, Lai Mohammed ya zargi kasar Ghana da muzguna wa ‘yan Nijeriya dake zaune a kasar da kuma tsananta masu a harkokin su na sana’a a kasar.

Ya ce baya ga wannan matsin, gwamnatin kasar da gangan ta rushe wani gini mallakin Nijeriya kuma ta kwace wani ginin da shi ma mallakin gwamnatin Nijeriya ne, sai dai mahukunta kasar Ghana sun karyata wadannan zarge-zarge.

Kojo Nkrumah, ya ce gine-ginen da Lai Mohammed ya ke magana a kai duk wa’adin da aka ba Nijeriya na mallakar su sun cika shekaru da dama da su ka wuce, kuma Nijeriya ba ta je ta sabunta damar ci-gaba da mallakar gine-ginen ba.

Ya ce ba gaskiya ba ne cewa su na dawo da ‘yan Nijeriya haka kawai tare da yi masu tsanani a wajen yanke masu hukunci, ya na mai cewa, shugabannin kasashen biyu za su gana nan ba da dadewa ba don a samu natsuwa a tsakani.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *