Kungiyar dattawan arewacin Nijeriya, ta yi watsi da wata gayyata da wani kwamitin wucin gadi na majalisar dattawa ya yi wa ‘yan Nijeriya don su bayyana ra’ayin su game da shirin gyaran kundin tsarin mulkin Nijeriya.

Ta ce majalisar ta na so ne kawai ta bata lokacin ‘yan Nijeriya ba tare da ta aiwatar da abubuwan da su ka dace ba.

Kungiyar dattawan, wadda ta yi kira ga sauran kungiyoyin farar hula na yankin su kaurace wa gayyatar da majalisar dattawan ta yi, ta ce a ganin ta duk wani shirin gyaran kundin tsarin mulki da za a yi bata lokaci da kudade ne kawai.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *