Tanzanian main opposition chief Tundu Lissu gestures from his wheelchair on January 5, 2018 in Nairobi, as he is wheeled by a supporter from a press conference to the hospital where he was admitted after being shot and critically injured at his home in September 2017. (Photo by TONY KARUMBA / AFP) (Photo credit should read TONY KARUMBA/AFP via Getty Images)

‘Yan adawa a Tanzania sun zargi gwamnati da yin coge yayin yiwa ‘yan takararsu rijistar shiga takara a zabukan kasar dake tafe a karshen watan Oktoba.

Jagoran ‘yan adawa a kasar ta Tanzania Tundu Lissu, yace yanzu haka gwamman ‘yan takara ne hukumar zaben kasar ta ki baiwa damar shiga zaben dake tafe, domin rashin adalci kawai, ba tare da kwararan dalilai ba.

A cewar Lissu ‘yan adawa na da jumillar ‘yan takara dubu 3 da 754 a zaben kananan hukumomi amma hukumar zabe ta yi watsi da kashi 30 daga ciki, sai kuma ‘yan takarar kujerun majalisar kasar 53 da aka zaftare daga cikin 244.

A watan jiya Tundu Lissu, ya koma Tanzani daga Belgium, inda ya shafe shekaru yana gudun hijira, bayan tsallake riiya da baya a shekarar 2017, lokacin da ‘yan bindiga suka yi yunkurin halaka shi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *