Tsohon shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya yi wa Shugaba Cyril Ramaphosa kakkausar suka mai ban mamaki.

A cikin wata wasiƙa da aka kwarmata, Mista Zuma ya ce Shugaban da ya gaje shi ya butulce wa jam’iyyarsu ta ANC mai mulkin ƙasar, kuma yana yi wa turawan ƙasar aiki ne.

Wannan matakin na tsohon shugaban ƙasar ya bayar da mamaki, duk da cewa jam’iyyar ta ANC ta dare gida biyu saboda rikicin cikin gida.

Mista Zuma ya kuma zargi shugaban ƙasar da wofintar da kaburburan “matasa maza da mata da jami’an tsaron gwamnatin nuna bambancin launin fata da ƴan barandansu suka kashe su”.

Ya kuma ce Mista Ramaphosa na butulcewa jam’iyyar ta ANC domin ya tsira da rayuwarsa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *