Makarantu za su koma karatu daga ranar 14 ga watan Satumba a Jihar Legas, bayan rufe su sakamakon bullar cutar coronavirus tun a watan Fabrairu.

Gwamna Babajide Sanwo-Olu, na jihar ya sanar cewa jihar za ta bude manyan makarantu a ranar 14 ga watan Satumba, kafin makarantun firarmare da sakandare da akwai yiwuwar bude su a  ranar 21 ga watan na Satumba.

Ya ce yana farin cikin sanar da cewa za a bar dukkan manyan makarantu su bude daga ranar 14 ga Satumba, 2020.

Game da makarantun firamare da sakandare kuma, y ace ana kokaringanin an bude su a ranar 21 ga watan Satumba, 2020.

Amman yace za a iya sauyawa gwargwadon abun da Ma’aikatar Lafiya da ke lura da yadda ake bin matakan kariyar cutar ta lura.

Tun a watan Maris gwamnati ta rufe makarantu a fadin Najeriya a kokarin dakile yaduwar cutar coronavirus, wadda ta fara bulla a Jihar Legas a Najeriya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *