Kungiyar Boko haram ta kashe mutane 2 tare da sace wasu, yayin farmakin da suka kaiwa manoma a wajen birnin Maiduguri.

Jami’an tsaron sa kai na Civilian JTF sun shaidawa kamfanin dillancin labaran AFP cewar, mayakan na Boko Haram sun afkawa manoman ne yayinda suke tsaka da aiki a kauyen Alau, a Juma’ar da ta gabata, inda suka sace 2 daga cikinsu bayan yiwa wasu 2 kisan gilla, ta hanyar sassara su da wuka.

Babakura Kolo daya daga cikin jami’an tsaron Civilian JTF yace manaoman sun fito ne daga wani sansanin ‘yan gudun hijira dake wajen birnin Maiduguri, inda suke noman.

Akalla mutane miliyan 2 rikicin Boko Haram ya raba muhallansu cikin shekaru 10, inda mafi akasarinsu a yanzu ke rayuwa a sansanonin ‘yan gudun hijira da suka dogara wajen samun tallafin kayayyakin abinci da magunguna daga hukumomin agaji.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *