Ministan kimiyya da fasaha, Dakta Ogbonnaya Onu, ya ce Kimiyya da fasaha na da matukar mahimanci a yaki da cin hanci da rashawa gwamnatin keyi a halin yanzun.

Ministan ya bayyana haka ne yayin da shugabanin kwamitin yaki da cin hanci da rashawa na kasa ‘National Anti-Corruption Marathon 2020’ suka kawo masa ziyara a ofishin sa a nan Abuja.

Ya ce, tabattar da bayanai na sirri akan cin hanci da yadda za a gabatar da aldalci a shari’un cin hanci da ake yi na bukatar sanya fasahar kimmiyya.

Ya kuma bayyana cewa, cin hanci da rashawa ta yi matukar durkushe cigaban kasa ta yada harkokin rayuwar ‘yan Nijeriya sun koma baya matuka.

Ya ce, ma’aikatar sa na goyon bayan kokarin da shugaban kasa Muhammadu Bujari, yake yi a yaki da ta’addanci da kuma yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *