Tsohon Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubakar Keita ya koma mazaunin sa a Bamako babban birnin Kasar kwana daya bayan da aka sako shi daga wani sansanin soji a Kita.

Kwamitin sojin da ke Mulki a kasar da ake kira NCSP ya tsare Keita, a lokacin da aka yi juyin mulki a kasar a makon da ya gabata, inda Keita, ya sanar da cewa ya yi murabus jim kadan bayan aukuwar lamarin.A lokacin da ya ke tsare, an bada rahoton cewa Keita, ya ce ba tilasta ma shi aka yi ya sauka daga kan karagar mulki ba, kuma ba ya so ya koma, amma ya na so a koma wa tsarin dimokradiyya cikin kankanin lokaci.

Majalisar Dinkin Duniya, tare da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWA, ne suka bukaci a saki Keita.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *