Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da nada shugabannin sabuwar hukumar kula da mabukata ta kasa. 

An kafa sabuwar hukumar ta kula da masu nakasa da ke bukatar kulawa ta musamman ne bisa tanadin dokar yaki da kyamar masu nakasa ta shekara 2019.

Tsohon dan majalisar wakilai daga Jihar Kebbi Husseini Suleiman Kangiwa, shi ne sabon shugaban hukumar, a yayin da aka nada Abba Ibrahim a matsayin Sakatare.

Wannan hukumar na da manufar kula da masu larura ta musamman da yawan su ya kai miliyan 25 a Najeriya, ta hanyar samar da karin kashi 5 cikin dari na aiyukan yi, da kuma ba su kulawa ta musamman akan batutuwan da suka dame su a dukan fanoni na rayuwa da kiwon lafiya da kuma harkokin walwalar su da nufin share masu hawaye.

Daya daga cikin shugabanin kungiyoyin masu larurar na kasa Misbahu Lawal Didi, ya ce yanzu ne masu fama da nakasa za su fara samun damar shiga a dama da su a harkokin mulki a Najeriya.

Misbahu ya yaba da wanan kokari da Gwamnati ta yi, wanda ya ce dama sun dade suna jiran irin sa, domin ba mutanen su damar ba da ta su gudummuwa a harkokin cigaban kasa, wanda hukumar za ta taimaka masu gaya wajen cimma wannan burin.

Shugabar mata masu larurar nakasar, Rabi Yusuf Gezawa, ta ce za su ci gaba da fafutukar tabbatar da ba a bar mata a baya ba wajen cin gajiyar hukumar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *