Sojojin Mali da suka yi juyin mulki a makon da ya gabata sun ɗaga ganawar da aka shirya za su yi a yau Asabar, irinta ta farko game da mayar da mulki ga farar hula.

Rahoton AFP ya ce sojojin sun ce ganawar da aka gayyaci ƙungiyoyin fararen hula daba-daban da suka haɗa da tsofaffin ‘yan tawaye da jam’iyyun siyasa domin tattaunawar an ɗaga ne saboda shirye-shirye.

Sai dai ba a gayyaci gamayyar ƙungiyar M5-RFP ba, wadda ta shirya zanga-zangar da ta yi sanadiyyar tilasta wa Boubacar Keita sauka daga kan mulkin sa, duk da cewa ta nace cewa sai an ba ta gurbi a gwamnatin riƙon ƙwarya.

Wasu sojoji masu ƙarancin shekaru da muƙami ne dai suka hamɓarar da Ibrahim Boubacar Keita daga muƙamin sa ranar 18 ga watan Agusta, inda suka tsare shi tare da mataimakin sa da sauran shugabanni.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *