Ministan Yaɗa Labarai da al’adu Lai Mohammed, ya ce Najeriya na duba hanyoyin ɗaukar matakan martani ga kasar Ghana.

Najeriya ta zargi Ghana kan abin da ta kira cin zarafin ‘yan Najeriya a Ghana da kuma yadda hukumomin Ghanar ke ƙara matsa wa ‘yan Najeriya lamba.

Wata sanarwa da ministan yada labaran, Lai Mohammed, ya bayar ta ce an mayar da ‘yan Najeriya a Ghana wasu abin yi wa ba’a. yana mai cewa gwamnatin Najeriya na duba hanyoyin da za ta bi domin yi wa tufkar hanci.

A cewar sa, rashin kyautawar da Ghana ta yi wa Najeriya sun hada da, rushe wani gini na ofishin jakadanacin Najeriya a birnin Accra, da ingiza ƙeyar ‘yan Najeriya zuwa gida da rufe shagunan su.

Shi ma ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama, ya ce farmakin da ake kai wa masu kasuwanci a Ghana ana yi ne saboda ƙoƙarin cimma manufar siyasa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *