Hukumar hana ayyukan cin hanci da rashawa da sauran laifuka masu jibi da haka ICPC ta kaddamar da bincike kan hukumar raya yankin Neja-Delta NDDC game da zargin karkatar da kuɗi Naira biliyan biyar.

Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a yau Asabar ta ce ta karɓi ƙorafi daga wasu ‘yan Najeriya kan shugabannin NDDC game da kuɗin kwangilar sayo kayan kariya daga cutar korona.

Ana binciken manyan shugabannin hukumar ne kan hannun da suke da shi a zargin karkatar da Naira biliyan 5 da miliyan 474 domin sayo kayan kariya daga annobar korona ga ma’aikatan lafiya a jihohi tara da nukumar NDDC ke kula da su.

Kazalika, ana binke kan kuɗin da hukumar ta kashe wurin ba ma’aikatan ta horo a ƙasashen waje yayin da ake tsaka da annobar korona.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *