Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani Kayode ya ce ya yi abun kunya ga kan sa da iyalan sa kan cin mutuncin da ya yi wa wakilin jaridar Daily Trust, Eyo Charles a bainar jama’a.

Ya shaida wa taron ‘yan jarida cewa ya yi matukar nadamar munanan kalamai da barazanar da ya yi wa Charles. tare da rokon dan jaridar ya yafe masa cin zarafin da ya yi masa kan tambayar da Charles, ya yi a lokacin wanin taron ‘yan jarida.

Fani-Kayode, ya ce yana rokon dan jaridar ya yafe masa, domin ya yi abun kunya ga kan sa da iyalain sa da abokan sa da abokan aiki har ma da iyayen gidan sa da ke ganin sa da kima sosai.

Ya ce yana matukar takaicin abinda ya yi wa dan jaridar ta yadda ya zafafa masa sosai bayan tambayar da ya yi masa akwai dan zolaya a ciki amma sai ya harzuka.

A wani taron ‘yan jarida da aka shirya wa tsohon ministan wanda ke zagayen duba ayyukan gwamnoni a yankin Kudu ne Charles, ya tambaye shi manufar ziyarar duba ayyukan gwamnonin da kuma mai daukar nauyin tafiye-tafiyen sa.

Bullar bidiyon irin cin mutuncin da ya yi wa dan jaridar, wanda bai tanka masa ba, ya ja wa tsohon ministan Allah-wadai daga ko’ina tare da neman ya janye dukkannin kalamai da barazanar sa ga Charles.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *