Ministar jin-kai da bunkasa rayuwa Sadiya Umar Farouq, ta amince a biya ma’aikatan shirin N-Power da aka sallama kudaden su.

A ranar Litinin da ta gabata ne, Ministar ta amince a biya basussukan da tsofaffin ma’aikatan ke bi wadanda ke rukunin farko da na biyu.

Tuni dai an tura bukatar biyan basussukan zuwa watan Yuni na shekara ta 2020 ga ofishin babban akan ta na kasa domin kammala bincike da biyan kudaden.

Yanzu haka dai kudaden watan Yuli na wasu daga cikin ‘yan rukuni na biyu ne ba a kai ga biya ba, kuma bukatar ta na gaban ofishin Babban akanta na kasa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *