Kungiyar ‘yan Jarida ta Nijeriya NUJ, reshen jihar Akwa Ibom, ta umurci ‘ya’yan ta su ƙaurace wa taron manema labaran da tsohon ministan sufurin jiragen sama Femi Fani-Kayode ya kira.

Wannan kuwa ya na zuwa ne, kwanaki kadan bayan bullar bidiyon tsohon ministan ya na zagin ɗan jaridar Daily Trust Eyo Charles saboda ya yi ma shi tambaya.

Eyo dai ya tambayi ministan cewa wanene ya ke ɗaukar ɗawainiyar tafiye-tafiyen da ya yi zuwa jihohin PDP, inda Fani-Kayode ya riƙa furta ma shi kalaman cin mutunci.

Da farko dai tsohon ministan ya ce bai zai ba kowa haƙuri ba, amma daga baya ya nemi afkuwar abokan sa da ke aiki a kafafen watsa labarai.

Duk da cewa akwai yiwuwar an yafe masa, amma har yanzu lamarin ya na yi ma wasu ‘yan jarida da dama zafi, inda ƙungiyar ‘yan jaridar ta ce kada wani ɗan jarida ya hallarci wani taro da tsohon ministan ya shirya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *