Shugaba Muhammadu Buhari ya kori Charles Dokubo, tare da maye gurbin sa da Milland Dikio a matsayin shugaban shirin Afuwa mai taken Amnesty Programme a turance.

Mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu, ya ce shugaba Buhari ya amince da nada Kanar Millan Dixion Dikio mai ritaya a matsayin sabon shugaban shirin.

Hakan kuwa ya biyo bayan amincewar shugaban kasa na sallamar Farfesa Charles Quarker Dokubo daga ofishin shugabancin hukumar cikin gaugawa sakamakon zarge-zargen da ake yi ma shi.

Garba Shehu, ya ce tuni an umurci Farfesa Dokubo ya mika dukkan takardun ofishin sa ga babban jami’in shirin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *