Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya goyi bayan kungiyar ECOWAS na ba sojojin kasar Mali wa’adin watanni 12 su mika mulki ga farar hula.

A ranar Juma’ar nan ne, shugaba Buhari ya halarci taron shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS na biyu ta yanar gizo na dangane da rikicin Mali  bisa jagorancin shugaban kungiyar Jean-Claude Kassi Brou.

Ana sa ran batutuwan da su ka tattauna su kasance a kan hanyoyin da za a kawo karshen rikicin siyasa da ya mamaye kasar ta Mali.

Bayanin hakan, ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasar shawara a kan kafofin sada zumunta Bashir Ahmad ya wallafa a shafin sa na Twitter.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *