Wani jirgi mai saukar Ungulu ya yi hatsari a Legas, inda aƙalla mutane biyu su ka mutu.

Bayanai sun ce jirgin ya faɗi ne a ginin wani Cocin sojoji a unguwar Opebi da ke Ikeja.

Wani bidiyo da ke yawo a kafofin sadarwa na yanar gizo, ya nuna yadda jirgin ya faɗi a rukunin gidajen.

Ana dai tunanin mutane hudu ne a cikin jirgin, kuma babu cikakken bayani game da yadda rayukan su ke ciki.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *