Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana damuwa a kan yadda karuwanci da ayyukan assha ke yawaita a sansanin ‘yan gudun hijra da ke Borno.

Zulumn ya bayyana haka ne, yayin da wata tawagar kwamitin harkokin musamman na majalisar dattawa ta ziyarce shi a karkashin jagorancin Sanata Yusuf Abubakar Yusuf a Maiduguri.

Rahotanni sun ce, kwamitin majalisar da ya kunshi Sanatoci 12, sun je jihar Borno ne domin duba ayyuka da nasarorin da hukumar ci-gaban yankin Arewa maso gabashin Nijeriya ta samu a jihar Borno da sauran jihohin da rikicin Boko Haram ya shafa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *