Gwamnatin tarayya ta amince da fitar da kudi Naira biliyan 10 a matsayin tallafi ga direbobi.

A cewar ministar zirga zirga na cikin gida, Sanata Gbemisola Saraki, tallafin zai taimaka wajen rage wahalhalun da direbobin ke fuskanta a dalilin annobar COVID-19.

Ministar tace tana kan tattaunawa da ma’aikatar ayyuka da gidaje dangane da hanyoyin da za a bi don samun kudaden shiga ta fuskar zirga-zirga.

Ta yi nuni da cewa yanzu haka kudaden na a hannun ma’aikatar masana’antu, da kasuwanci, tana mai cewa ma’aikatar ta na kan shirye-shiryen rabon kudade.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *