Yan Takara 14 ne zasu fafata da shugaban kasar Tanzania John Magufuli, a zaben da za’ayi a watan Oktoba mai zuwa wanda masu sa ido ke cewa zai bashi damar samun nasara ganin yadda ‘Yan adawa suka rarraba kan su.

Daga cikin masu fafatawa da shi harda Tundu Lissa, wanda ya koma kasar daga Belgium bayan ya kwahse shekaru 3 yana jinyar harbin da aka masa, sai tsohon ministan harkokin waje Bernard Membe, da aka kora daga cikin Jam’iyyar Chama-cha Mapinduzi a watan Fabarariru.

Ana sa ran gudanar da zaben ne ranar 28 ga watan Oktoba, yayin da ga alama ‘yan adawar zasu fuskance shi ba tare da hadin kai ba.

A wannan karon ‘yan adawa a kasar ta Tanzania na tunkarar zabukan na shugaban kasa da ‘yan majalisu ne ba tare da kulla kawancen da ya basu damar lashe kaso mai yawa na kuri’un da aka kada a manyan zabukan ba a shekarar 2015, lokacin da shugaba mai ci John Magufuli ya lashe zaben shugabancin kasar zangon farko.

‘Yan adawar da masu rajin kare hakkin dan adam na zargin Magufuli da yin amfani da karfin mulki wajen hana ‘yancin fadin albarkacin baki, da takura kafafen yada labarai.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *