Shugaba Muhammadu Buhari, ya taya Dr. Akinwunmi Adesina, murnar sake zaɓar sa Shugaban Bankin raya yankin Afirka karo na biyu.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan yaɗa labarai Femi Adesina, ya fitar a nan Abuja.

Sanarwar ta ce Shugaba Buhari, ya samu labarin ne a yayin da yake tsaka da taron da ya haɗa da shugaban majalisar dattawa da wasu ministoci da manyan jami’an gwamnati.

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, ne ya isar da sakon ga Shugaba Buhari, inda ya yi tafi taya murna yana mai cewa ya cancanta.

Shugaba Buhari, ya miƙa saƙon godiya ga Ƙungiyar Tarayyar Afrika don zaɓen da ta yi wa Adesina.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *