Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sunusi 11 ya ce ba zai taba zama dan wata jam’iyyar siyasa ba saboda shi shugaban Al’umma ne wanda yake da magoya baya acikin kowace jam’iyyar siyasa a fadin Najeriya

Sarkin kanon na 14 ya bayyana hakan ne cikin ziyarar da yakai jihar Kaduna bayan da wasu ke ta kiraye-kirayen da ya fito takara a zaben shekara ta 2023.

 Ya kara da cewar a matsayin sa na uban kasa yana da abokai da mabiya a cikin kowace jam’iyya saboda haka ba zai zama dan wata jam’iyya ba.

Yana mai cewar shawarar da zai ba ‘yan Najeriya shine idan suka tabbatar da ingancin wani dan takara su mara masa baya ba tare da nuna babbancin jam’iyyar da ya fito ba, kuma ba shugaban kasa kadai ne zai iya kawo sauyi mai ma’ana ba har ma da gwamnoni, da ‘yan majalisun dokoki da kuma shugabannin kananan hukumomi.

Muhammadu Sunusi, na 2 yace lokaci yayi da matasa masu jini a jika za su taso a fafata da su.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *