This Friday Oct. 31, 2014 image taken from video by Nigeria’s Boko Haram terrorist network, the leader of Nigeria’s Islamic extremist group Boko Haram, center, has denied agreeing to any cease-fire with the government and said Friday more than 200 kidnapped schoolgirls all have converted to Islam and been married off. AP/PTI(AP11_1_2014_000109B)

Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar shiyyar Borno ta Kudu, Sanata Ali Ndume, ya bayyana cewar mayakan Boko Haram sun yiwa dattijan dake karamar hukumar Gwoza 75 yankan rago a dare guda.

Dan majalisar ya kara da cewar bayaga dattijan da suka halaka a watannin baya lokacin da suke kan ganiyar kai hare-hare a sassan jihar Borno, mayakan na Boko Haram sun kuma yiwa matasa da dama kisan gilla a yankin na Gwoza, ta hanyar sanya su yin layi, inda suka kuma rika bi suna harbewa daya bayan daya.

Yayin da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki da Majalisar ta shirya kan rikici na baya bayan nan, Sanata Ndume, yace har ya zuwa wannan lokaci yankin sa na Gwoza na fama da matsalar tsaron da ba zai iya zuwa wurin ba.

Dan Majalisar wanda ya yabawa sojoji kan kokarin da suke, yace har yanzu rikicin Boko Haram bai kare ba, ganin yadda suke cigaba da hallaka mutane a Jihar sa.

Sanata Ndume ya kuma koka kan cewar har yanzu dubban al’ummar jihar Borno da sauran sassan yankin arewa maso gabashin Najeriya na fama da matsalar yunwa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *