Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya taya Kaycee Madu, wani dan Najeriya murnar nada shi matsayin Ministan shari’a kuma babban jami’in shari’ar gwamnatin lardin Alberta a kasar Canada.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da ta samu saanya hannun mai taimaka wa Shugaban kasa shawara na musamman, Femi Adesina, ya raba a nan Abuja.

Ya ce Kaycee Madu, ya kafa tarihi a matsayin dan Afrika da aka nada Ministan lardi a tarihin Canada, kuma shine Sakataren lardi da ke rike da hatimin lardin Alberta.

Shugaba Buhari, ya bayyana wannan karramawar a matsayin gagarumar nasara ya na mai cewa hakan ya sake karrama ‘yan Najeriya a matsayin masu hazaka, da ke bayyana kan su ta fannonin rayuwa dabam daban.

Shugaban kasa ya ce a matayin sa bakar fata na farko da aka ba mukamin Ministan shari’a kuma Attoni janar a Canada, Madu ya shiga littattafan tarihi, sai ya yi kira ga ‘yan Najeriya, a gida da waje, su ci gaba da kasancewa wakilan kasa rsu na gari.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *