Shugabar hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya NAFDAC, Mojisola Adeyeye, ta ce ta tarar da bashin naira billiyan uku da miliyan dari biyu a lokacin da ta kama aiki a shekarar 2017.

Adeyeye ta bayyana hakan  ne a wajen taron manema labarai da hukumar ta shirya kan aikace-aikacen da tayi da kuma wadanda ta sanya a gaba.

Shugabar hukumar wanda ta ce tuni an biya bashin, ta kara da cewa hukumar ta samar da kudaden shiga da yawansu ya kai naira billiyan bakwai a shekarar ta 2017.

Ta kara da cewa hukumar ta kuma samar da naira billiyan 2 da milliyan dari biyar da naira billiyan 3 da milliyan dari a shekarar 2018 da kuma 2019.

Ta kara da cewa hukumar na ci gaba da aiki ba dare ba rana na ganin ta cimma nasara a duk abubuwan da ta sanya a gaba musamman na tabbatar da ingantattun kayayyakin abinci da magunguna ga ‘yan Najeriya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *