Babban Sufetan ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu, ya bukaci masu hannu da shuni da kungiyoyi su rika tallafawa rundunar a kokarin da take na sauke nauyin dake kanta.

Jami’in yada labarai da hulda da jama’a na rundunar Frank Mba, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Ya ce Sufetan ‘yan sandan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi kyautar wasu motocin aiki da wani kamfani ya ba rundunar domin inganta aikace-aikacen ta.

Sufetan ‘yan sandan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa dake kula da aikace-aikace Abdulmajid Ali, ya ce za a yi amfani da motocin ne wajen inganta aikace-aikacen jami’an ‘yan sanda ake aiki a cikin al’umma.

Ya ce rundunar na ci gaba da karbar tallafi daga gwamnatoci, hukumomi, bangarori masu zaman kansu da wasu masu hannu da shuni domin inganta shirin.

Adamu ya ce tallafin da rundunar ke samu daga bagarori daban-daban zai taimaka wajen bunkasa shirin ta na kara zage damtse na tsaron lafiya da dukiyoyin al’umma.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *