Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce jam’iyyu 13 cikin 18 masu rijista sun bayyana shirin sun a yin zaben fidda dan takara a zabukkan cike gurbi da za a yi guda goma sha 2 dake fadin kasar nan.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ta samu sanya hannun babban jami’in yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a Festus Okoye, jim kadan bayan taron da hukumar ta gudanar a Abuja.

Okoyo y ace dukkanin jam’iyyun da suka bayyana shirin nasu sun ce za su yi amfani da tsarin wakilan jam’iyyu ne wajen zabo ‘yan takaran da za su tsaida.

Sai dai ya ce wasu daga cikin jam’iyyun basu bayyana inda za su gudanar da zabubbukan ba.

Ya ce tun a ranar 11 ga wannan watan da muke ciki hukumar ta fitar da jadawalin yadda zata gudanar da zabubbukan cike gurbin guda 12.

Okoye ya kara da cewa za a gudanar da zabukkan ne ranar 31 ga watan Oktoba a jihohi 8 dake fadin kasar nan.

Ya ce shugabannin majalisun dokokin jihohin Enugu da Katsina sun sanar da hukumar mutuwar ‘yan majalisu dake wakiltar Isi-Uzo a Enugu da kuma Bakori dake jihar Katsina.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *