Hukumar kula da ingancin kayayyaki ta Najeriya SON ta lalata tukwanen iskar da rufin kwano da kudinsu ya kai naira milliyan dari 4 da 50.

Babban jami’in sashen tabbatar da ka’ida na hukumar Obiora Manafa, ya bayyana haka a lokacin lalata kayayyakin na bogi a Legas.

Ya ce kayayyakin da aka lalata na da hadarin gaske ga rayuwar al’umma idan aka yi amfani dasu a gidaje.

Manafa ya kara da cewa duk kokarin da hukumar take na dakile safarar kayayyaki makamantan haka, mutanen sun san duk hanyoyin da suka bi wajen shigo da kayayyakin.

Ya kuma jaddada kudurin hukumar na yin dukkanin mai yiwuwa tare da zakulo kayayyakin da ake shigo dasu wadanda basu da ingancin da ake bukata.

Manafa ya kara da cewa an kwato kayayyakin ne a wuraren ajiya wasu kuma akan hanyoyi da ake tafiya dasu zuwa wasu sassan Najeriya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *