Mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin aikin noma Andrew Kwasari, ya bukaci ‘yan Najeriya su kara hakuri da gwamnatin tarayya a kokarin da take na sake gina kasa.

Kwasari ya bayyana hakan  ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a babban birnin tarayya Abuja.

Ya kuma bada misalai da aikace-aikacen da gwamnatin tarayya ta yi da kuma wadanda take yi domin jin dadin ‘yan Najeriya, musamman a wannan lokaci na annobar korona.

Ya kuma jaddada nagarta da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ke da shi, wanda a cewarsa ba karamar dama bace ga Najeriya na samar da ci gaba.

Kwasari ya kuma koka kan tasirin cin hanci da rashawa a Najeriya, tare da kyautata zaton Najeriya za ta maido da darajar da take dashi da kuma kima a sauran kasashen duniya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *