Gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmad El-Rufai ya yabawa kungiyoyin tabbatar da zaman lafiya karkashin jagorancin shugabannin al’umma a karamar hukumar Zangon Kataf.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da tawagar karkashin jagorancin Agwatyap Dominic Yahaya, ta kai masa ziyara tare da bayyana matsayar da aka cimma a taron zaman lafiya da aka gudanar ranar Asabar din da ta gabata.

Taron wanda ya kunshi Hausawa, Fulani da ‘yan kabilar Atyap an cimma matsayar sanya hannu a yarjejeniyoyi 14 da aka cimma na zaman lafiya.

Gwamnan ya ce hanya daya tilo da za a iya samun dauwamammiyar zaman lafiya a yankin shine idan al’ummomin yankin sun amince su zauna lafiya da junansu.

Ya ce hadin kan al’ummomin jihar na da matukar muhimmanci a kokarin da gwamnatin da hukumomin tsaro ke yi wajen samar da zaman lafiya.

Sannan ya bukaci al’ummomin jihar su rungumi zaman lafiya kamar yadda aka cimma matsaya, tare da ba hukumomin tsaro hadin kai wajen tabbatar da tsaro.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *