Kungiyar rainon tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta bukaci sojojin da suka yi juyin mulki a kasar Mali su bada damar gudanar da zaben da zai mayar da mulki a hannun farar hula nan da shekara guda.

Sanarwar wacce ta fito ta fadar shugaban Najeriya ta ce watanni 12 zasu ba gwamnatin rikon kwaryar damar shirya karbabben zaben da zai dora fararen hula a mulki.

Wannan na daga cikin abinda shugaban tawagar Goodluck Jonathan ya shaida wa shugaba Muhammadu Buhari lokacin da yayi masa bayani kan ziyarar da suka kai Mali da kuma tattaunawar da suka yi da bangarorin dake rikici a  kasar.

Sai dai sojojin da suka yi juyin mulkin sun ki amincewa da bukatar mika mulki cikin shekara guda, inda suka ce suna bukatar shekaru 3 domin tabbatar da cewar al’amura sun koma daidai.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *