Runduna ta musamman dake yaki da ayyukan ta’addanci a yankin arewa maso yammacin Najeriya ta gano wajen hakar ma’adanai na bogi a jihar Zamfara.

Mai rikon mukamin mai magana da yawun rundunar Birgadiya Janar Benard Onyeuko, ya bayyana haka a wani taron manema labarai a sansanin dake Faskari.

Ya ce ‘yan ta’adda da suka addabi yankin na amfani da sansanin dake karamar hukumar Bukuyyum domin boyewa a duk lokacin da suke shirye-shiryen kai hari.

A samamen da jami’an sojin suka  kai sun kama ‘yan ta’adda akalla 150 tare da kwato wasu bindigogi kirar hannu guda 20.

Onyeuko, ya ce runduna ta kuma kashe daya daga cikin wadanda ake zargi ‘yan ta’adda ne a lokacin da ya yi yunkurin guduwa. 

Ya kara da cewa binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa baya ga yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba na tallafawa ayyukan ta’addanci. 

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *