Ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi mai murabus ya ce, ya sha alwashin cika wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, babban burinsa na tabbatar da cewa, gwamnati ta kawo karshen matsalar tsaro a fadin Najeriya baki daya.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ta samu sa hannun mai taimaka ma sa kan harkokin yada labarai, Mohammad Abdulkadir, kan cikar sa shekara daya a matsayin ministan, wanda ya raba a nan Abuja.

Ya ce zai yi haka ne kasancewar shugaba Buhari, shi ne babban kwamandan askarawan Najeriya, wanda ya sadaukar da kan sa ga kasa ba tare da son kai ko kasala ba.

Janar Magashi, ya kuma gode wa Shugaba Buhari, bisa damar da ya ba shi ta yi wa kasar sa ta haihuwa hidima, ya na mai cewa, yanzu ne ma su ka fara aiki tukuru ga Nijeriya da ’yan Nijeriya.

A yayin da ya ke tabbatar da irin goyon bayan da Shugaban Kasa yake ba rundunonin sojin Najeriya don kawo karshen matsalolin tsaron da su ka shafi na ’yan tayar da kayar baya, da satar mutane da kuma sauran ’yan ta’adda, Janar Magashi, ya bayyana kwarin gwiwarsa da cewa, lallai haske na nan tafe a karshen al’amarin.

Ya yi kira ga dukkan shugabannin rundunonin tsaron Najeriya su sake tashi tsaye wajen nuna kishin kasa, tare da yin aiki tare, domin nauyi ne wanda ya rataya a wuyan dukkan ’yan Nijeriya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *