Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi amfani da tattaunawa da kuma tafarkin siyasa wajen shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi Najeriya.

Babban Jakadan Majalisar a Najeriya Edward Kallon, ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci wata tawaga zuwa fadar shugaban, inda ya ke cewa matsalolin tsaron da suka addabi kasa da ke da rassa daban daban na da wahalar magance su.

Kallon, ya ce yayinda sojoji su ke fafatawa, yana da matukar muhimmanci a goya musu baya wajen tattaunawa da amfani da hanyar siyasa domin samun zaman lafiya.

Jami’in ya bayyana matsalolin da suka addabi Najeriya guda 3 da suka hada da matsalar zama dan kasa da mallakar dukiyar kasa da kuma rikicin shugabanci.

Kallon ya ce Majalisar na kashe akalla Dala biliyan guda da rabi kowacce shekara wajen gudanar da ayyukan jinkai a Najeriya, musamman a yankin da ake fama da rikicin boko haram.

Jami’in ya yabawa shugaba Buhari, kan rawar da ya ke takawa wajen yaki da cin hanci da rashawa da kwato dukiyar jama’a tare da kuma sake fasalin ayyukan gwamnati, inda ya bukaci shugaban ya fadada wajen sanya hannu mazauna yankunan karkara cikin yakin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *