Kungiyar gwamnonin Arewa NGF ta yaba wa Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, yayin da yake cika shekara 64 da haihuwa.

Kungiyar ta ce irin ayyukan wanzar da zaman lafiya da kokarin magance jahilci a yankin Arewa da sarkin musulmi yaka yi ya cancanci yabo.

Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya bayyana haka a sakon taya murna da Daraktan yada labaran sa, Makut Simon Macham, ya fitar a Jos.

Ya yaba da kokarin sarkin musulmi na inganta zaman lafiya, da hadin kai da cigaba a Arewa da ma kasa baki daya.

Ya ce ‘yan Arewa na alfahari da irin tallafin suke samu daga wurin sarkin na shawo kan kalubalen dake damun yankin Arewa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *