Gwamnatin  tarayya ta ware kudi Naira biliyan 126 don inganta asibitoci a fadin Najeriya.

Asibitocin da za a gyara sun hada da asibitin FMC, da dakunan gwaje-gwajen cututtuka, da sashen kula da masu bukatar kula ta gaggawa, da sashen da ake kebe masu fama da cututtukan da ba a son sauran mutane su Kamu, da asibitocin koyarwa dake jihohin 36 na Najeriya.

A shekararun baya ne wasu kwararru a fannin kiwon lafiya suka yi kira ga gwamnati kan hada hannu wajen ware isassun kudade domin inganta fannin kiwon lafiya.

Kwararrun sun yi wannan kiran ne a taron samun madafa kan samar da kiwon lafiya mai nagarta ga mutane cikin sauki da aka yi a  nan Abuja.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *