Karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, ya ba daliban Najeriya tabbacin cewa bada jimawa ba ne za a bude makarantun gaba da sakandare a fadin Najeriya baki daya.

Ya ce duk da cewar ba’a bayyana ainahin ranar da za a bude makarantun ba, ya bukaci dalibai su sha kurumin su.

Ya bayyana cewa ma’aikatar ilimi na aiki domin samun rahoto daga hukumar kula Jami’o’i ta Najeriya NUC da sauran hukumomi na makarantun gaba da sakandare daban daban.

Karamin ministan ya ce bayan sun samu rahoton za su gabatar ga kwamitin fadar shugaban kasa kan yaki da annobar korona domin dubawa.

Nwajiuba, wanda ya bayyana hakan yayinda yake amsa tambayoyi a wani taro a nan Abuja, ya kara da cewar ma’aikatar tana samu kira daga jami’o’i masu zaman kansu da jami’o’in gwamnati don sake bude makarantun.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *